Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHarin Kaduna: Majalisar wakilai ta gayyaci shugabanin tsaron kasar nan

Harin Kaduna: Majalisar wakilai ta gayyaci shugabanin tsaron kasar nan

Date:

Majalisar wakilai ta bukaci shugabannin tsaron kasar nan su bayyana a gabanta domin yin bayani kan harin Jirgin kasan Kaduna.

Majalisar ta bukaci shugabanin su bayyana a yau Alhamis domin karin bayani.

Sai dai tun a a jiya Larabar shugabannin tsaron suka nemi su gana da shugabancin majalisar ƙarƙashin Mataimakin Kakakin Majalisa Ahmed Idris Wase, amma sai majalisar ta ƙi yarda da hakan, tana mai tilasta musu bayyana a gabanta a yau Alhamis.

Majalisar dai na son hafsohin tsaron su yi mata ƙarin bayani ne g ame da yadda ‘yan fashi suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum takwas.

Kazalika, tana so ta ji yadda ‘yan bindigar suka kai wani harin kan filin jirgin sama na Kaduna kwana biyu kafin na jirgin ƙasan.

Waɗanda majalisar ke son su bayyana a gabanta sun haɗa da hafsoshin tsaron ƙasa, da sufeton ‘yan sanda na ƙasa, da ministocin da lamarin ya shafi ma’aikatunsu bisa umarnin shugabannin kwamatocin soja da na sufurin jirgin sama da na ‘yan sanda da na sufuri.

Ana sa ran za su bayyana da misalin karfe a3:00 na rana.

Latest stories

Related stories