Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan Najeriya miliyan 95 za su fada kangin talauci a 2022 —...

‘Yan Najeriya miliyan 95 za su fada kangin talauci a 2022 — Bankin Duniya

Date:

Bankin Duniya ya fitar da wani rahoto inda ya yi hasashen yawan talakawa a Najeriya zai karu zuwa mutum miliyan 95 nan da karshen 2022.

Wannan na dauke ne cikin wani rahoto da ya fitar don samar wa Najeriya makoma ta gari.

Ya ce rage radadin fatara ya samu koma baya tun a 2015, inda ’yan Najeriya da dama suka fada cikin kangin talauci na tsawon shekaru.

A cewar bankin, an yi hasashen adadin mutanen da za su fada cikin kuncin rayuwa a Najeriya zai kai miliyan 9.4 a karshen 2022.

Kazalika, ya ce rahoton wani kokari ne na neman hanyoyin fitar da ’yan Najeriya daga kangin rayuwa.

Wata kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa yawan talakawan Najeriya ya kai kashi 42.8 cikin 100 a 2020, wanda yana kasa da kididdiga ta 2010 da kuma ta 2011 da ya kai kashi 43.5 cikin 100.

Har wa yau, bankin ya ce akwai yiwuwar wadanda za su fada talauci ya haura idan aka yi la’akari da yadda yawan al’ummar Najeriya ke karuwa a kodayaushe.

Alkaluman da aka zayanna a baya-bayan nan sun ba da kiyasin cewa talauci ya fara raguwa a farkon 2010 sannan kuma ya sake ninkawa a 2015.

Sai dai wannan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da koma bayan tattalin arziki a 2016 sakamakon faduwar farashin mai a kasuwanin duniya.

Kazalika, rahoton ya ce bullar annobar COVID-19 ta daidaita tare da jefa sama da mutum miliyan biyar a Najeriya cikin kangin talauci.

Tuni kayan masarufi suka ninka kudinsu wajen sau hudu a Najeriya, lamarin da ya sanya masu karamin karfi shiga halin ni-’ya-su.

Lamarin ya kuma tagayyara rayuwar miliyoyin mutane, wasu da dama abin da za su ci na neman gagararsu, wanda hakan ya tilasta wasu shiga yin bara a manyan tituna da kuma lungu da sako na unguwanni.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...