Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZa a fara yiwa Jirgin kasa rakiya da Jirgin yaki-Ameachi

Za a fara yiwa Jirgin kasa rakiya da Jirgin yaki-Ameachi

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu jiragen sama ne za su dinga yi wa jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna rakiya da zarar ya ci gaba da aiki.

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara jihar don gane wa idonsa abin da ya faru.

Bayan ya duba waɗanda suka jikkata a Asibitin 44 na Sojoji a Kaduna, Amaechi ya kuma gana da Hafsan Sojojin Sama Air Marshal IO Amao da kuma Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

“Na faɗa wa hafsan sojan sama cewa idan muka gama gyaran layin dogo, jirgin zai ci gaba da aiki bisa rakiyar tsaro ta sama daga sojan sama har sai an saka kayayyakin tsaro daga nesa kamar yadda shugaban ƙasa ya ba da umarni,” in ji Amaechi cikin wani saƙon Twitter.

Ministan ya zargi “abokan aikinsa” cewa su ne ke hana ruwa gudu tun lokacin da ma’aikatarsa ta nemi kuɗin sayen kyamarorin tsaron a baya

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...