Saurari premier Radio
26.2 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDamuna:NIMET ta ce za a samu ambaliyar ruwa a kasar nan

Damuna:NIMET ta ce za a samu ambaliyar ruwa a kasar nan

Date:

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIMET) ta ce akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwan sama a wasu sassan kasar nan.

NINET ta ce abin zai fi shafar Jihar Taraba da yankin Kudu maso Yamma.

Babban Daraktan Hukumar na Kasa, Farfesa Mansur Matazu, ne ya sanar da hakan ga manema Labarai.

Ya ce sanarwa ta zamo dole, don al’ummar wadannan yankuna su mike tsaye domin tarar ambaliyar tun kafn hakan ta auku.

Yankuna da dama a kasar nan tuni suka fara samun amabliyar, kwanaki kadan bayan faduwar damuna.

Yankunan sun hadar da Legas da Bauchi Kano, inda aka samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.

Matazu ya ce tsawon shekaru 15 ke nan hasashen da Hukumar ke yi na tabbata da kusan kaso 95 cikin 100.

A cewarsa dokar tabbatuwar ingancin hasashen yanayi da Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya ta fitar shi ne samun tabbatuwarsa da kaso 65 cikin dari.

Haka zalika Daraktan ya koka kan yadda wasu gwamnatocin jihohi da kananan Hukumomi ke watsi da hasashen da Hukumar ta yi.

Wanna kuma yasa al’amuran na ci gaba da ta’azzara musamman ambaliyar idan ta zo.

Don haka ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su dinga bai wa hukumar muhimmacin da ya kamata domin rage karfin ambaliya a fadin kasar nan.

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...