32.2 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiTattalin ArzikiHukumar Kwastam Shiyyar Kano da Jigawa na Samarwa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan...

Hukumar Kwastam Shiyyar Kano da Jigawa na Samarwa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 4 Duk Wata

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Abdurrashid Hussain

Hukumar hana fasakwari ta kasa shiyyar Kano da Jigawa tace tana samarwa gwamnatin tarayya naira milliyan dubu hudu a matsayin kudaden haraji a kowanne wata.

 

Sabon kwanturolan hukumar Mu’azu Hassan Raji ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci fadar sarkin Kano.

 

Ya ce hukumar na alfahari da jihar Kano la’akari da irin ficen da ta yi ta fuskar kasuwanci musamman a yankin arewa.

 

Da yake jawabi, mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci jami’an hukumar da su zama masu fadakar da al’umma dokoki, tare da kira ga al’ummar jihar Kano da su zama masu kokarin bin dokokin kasa, wanda yace hakan zai samar da zaman lafiya a tsakanin mutane.

 

Sabon shugaban hukumar ya kuma ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin ya gabatar da kansa da samun hadin kan masarautar da kuma goyon baya domin samun nasarar aiwatar da aikin da aka turo shi yi jihar nan.

Latest stories