27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiWani dan kasar China ya kashe wata budurwa a Kano

Wani dan kasar China ya kashe wata budurwa a Kano

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

 

Wani Dan kasar China Geng Quanrong ya kashe wata budurwa Mai suna Ummukulsum Sani ta hanyar caccaka mata wuka.

 

Acewar Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano Lamarin ya faru ne a unguwar Dorayi Babba da ke nan Kano.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa Premier Radio cewa Dan Chinan Mai shekaru 47 ya haura har gidan su ya rinyar ne ya kashe ta.

 

Dan Chinan dai na zargin Ummukulsum da yaudararsa, ta hanyar kin aurensa bayan ya Dade yana yi mata hidima.

 

Hakan ce ta Sanya ransa ya baciya kuma ya je har gidansu dake unguwar Yamadawa a Dorayi Babba ya kuma haura cikin gidan don aiwatar da mummunar manufarsa

 

Bayan ya haura ne ya shiga dakin yarinyar ta taga, ya zaro wuka ya fara caccaka mata a wuya da kafadunta.

 

A cewar Kiyawa bayan samun Labarin ne kwamishinan yan sandan Kano ya tura jami’ansa karkashin DPOn Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.

Ya ce da isarsu ne suka dauki yarinyar zuwa Asibitin Murtala inda likita ya tabbatar da da mutu.

Kiyawa ya ce tuni Suka damke wanda ake zargi kuma an mayar da shi shalkwatar Yan sandan domin ci gaba da bincike.

 

Bayan ya soka mata wukar ne kuma mahaifyarta ta yi ihun akawo taimako inda wami matashi ya yi kukan kura ya Kai dauki.

 

Kiyawa ya ce da samun Labarin ne kuma kwamishinan yan sandan ya tura jami’ansa karkashin DPOn Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.

 

Latest stories