Saurari premier Radio
25.6 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiOsinbajo Zai wakilci Najeriya a Jana'izar Sarauniya Ingila

Osinbajo Zai wakilci Najeriya a Jana’izar Sarauniya Ingila

Date:

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, zai wakilci Najeriya yayin jana’izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ll ta kasar Ingila.

Sarauniya Elizabeth ll ta rasu a ranar 8 ga watan Satumba a gidan ta na shakatawa na Balmoral dake Scotland ita ce sarauniyar da ta fi dadewa a kan sarautar Burtaniya.

 

Osinbajo zai bar Abuja ne a yau Asabar don halartar Jana’izar da zata haɗa da dangin sarauta, da shugabannin kasashen duniya ciki har da mambobin kungiyar Commonwealth,  firaministan kasashe,da aka shirya gudanarwa a Westminster Abbey dake birnin Landan a ranar Litinin.

 

Gabanin Jana’izar mataimakin shugaban kasar zai kasance cikin manyan baki da Sarki Charles lll da Sarauniya Camilla za su tarbe su, a wata liyafar da za a gabatar a fadar Buckingham, ranar Lahadi, a cewar wata sanarwa da sai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laolu Akande ya fitar.

 

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...