Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da hedikwatar Ƙungiyar Fansho ta Ƙasa (NUP) da ke Abuja da aka sakawa suna Comrade Godwin Abumisi Pensioners’ Legacy House, inda ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na inganta walwala da kare haƙƙin masu ritaya.
Yayin bikin, gwamnan ya kuma ba da tallafin Naira miliyan 100 ga ƙungiyar, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da biyan fansho da kuma ƙoƙarin kammala biyan bashin kuɗaɗen gatan masu ritaya kafin kare wa’adinta.
Shugaban ƙungiyar Fansho ta ƙasa, Kwamared Godwin Abumisi, ya yabawa gwamnatin Kano kan biyan Naira biliyan 32 daga cikin bashin Naira biliyan 48.6 da ta gada, tare da tuna cewa a shekarar 2024 an karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf da lambar yabo ta “Gwamnan da ya fi kula da masu ritaya.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta ƙara mafi ƙarancin kuɗin fansho daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000, domin rage wa masu ritaya raɗaɗin tsadar rayuwa.
A nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa ƙungiyoyin ƙwadago.
Daga bisani, shugabannin Ƙungiyar Fansho ta Ƙasa sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya sake yin takarar wa’adi na biyu a zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2027, sakamakon abin da suka bayyana a matsayin kyakkyawan aikin da gwamnatinsa ke yi a fannoni daban-daban.
