Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGirman aikin da matatar man Dangote zata nayi a kowacce rana.

Girman aikin da matatar man Dangote zata nayi a kowacce rana.

Date:

Kabiru Bello Tukur

 

Matatar danyen mai ta Dangote da zata fara aiki a yau Litinin, zata dinga tace ganga dubu Dari Shida da hamsin (650,000) a kowace rana.

 

Wannan zai taimaka wajen rage shigo da tataccen man cikin kasar nan da kusan Kashi tamanin.

 

Matatun gwamnatin tarayya na Porthacourt da Warri da kuma Kaduna idan aka hada su guri guda suna samar da ganga 445,000 kawai a rana, in har suna aiki yadda yakamata, wanda rabon da a ga hakan har an manta.

 

Hukumar Kididdiga ta kasa NBS tace ana amfani da lita miliyan 68 na man fetur a kowacce rana a Najeriya.

 

Domin fahimtar abun sosai, kowa ce ganga daya tana samar da kusan Lita 170, Saboda haka ganga 650,000 da matatar Dangote zata samar, zai Kai sama da Lita miliyan 50.

 

Gibin Lita miliyan 18 zai kasan ce ko dai matatun 3 na kasa su samar dashi Ko Kuma a cigaba da shigo dashi daga waje, wanda da wuya hakan ta yiwu ganin cewa akwai yiwuwar faduwar fashin man da zarar Matatar ta fara aiki ka’in da nau’in.

 

Dainawa ko kuma rage shigo da man zai sanya man da ake samarwa a nan cikin gida yayi sauki, kudin da kasar nan ke kashe wa kan tallafi ya tsira.

 

Haka kuma masana na ganin daina shigo da Mai zai taimaka wurin matasa su samu aikin yi, kana, sana’oin da suka durkushe Saboda tsada ko karancin man zasu farfado.

Wannan matatar Mai ta Dangote tuni ta samarwa da yan Najeriya ayyukan yi sama da Dubu 30.

 

Latest stories

Related stories