Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari na kaddamar da matatar Mai mafi girma a Afirka mallakin dan...

Buhari na kaddamar da matatar Mai mafi girma a Afirka mallakin dan asalin Kano.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar bikin kaddamar da matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afirka, Kuma guda cikin manyan matatun Mai a duniya.

 

Matatar mallakin hamshakin dan kasuwar nan, mafi kudi a Afirka kuma dan asalin Kano, zata na tace danyan mai a wannan kasa.

 

Matatar man da aka kashe kudin da ya haura Dala biliyan 20 ta shiga sahun manyan matatun Mai a duniya.

 

Ana ganin samar da matatar zai kawo karshen fitar da danyan mai da Najeriya keyi Don tacewa.

 

A jawabinshi hamshakin dan kasuwar ya ce wannan bikin kaddamarwa na zama tamkar wata kafa damba don cimma manufar habbaka tattalin arzikin kasar nan.

 

Matatar dai an ginata ne a jihar Lagas dake Najeriya.

Latest stories

Related stories