Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotun sauraran korafe-korafen zabe tayi watsi da bukatar Atiku da Obi ta...

Kotun sauraran korafe-korafen zabe tayi watsi da bukatar Atiku da Obi ta haska shari’a kai tsaye.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Jagoran alkalan kotun dake sauraran shari’ar kan zaben shugaban kasa na 2023 Mai shari’a Haruna Tsammani ne yayi watsi da bukatar yan takarar na jamiyyu PDP da LP.

Sun dai shigar da bukatar haska shari’ar zabe ne kai tsaye a kafafen yada labarai.

Mai shari’a Haruna yace jamiyyar PDP da LP sun gaza gamsar da kotun kuma bukatar tasu bata karbu ba.

A ranar 8 ga watan Mayu dai Atiku Abubakar dan takarar PDP ya shigar da bukatar neman a haska shari’ar kai tsaye.

Shima dan takarar LP Peter Obi ya biyo bayan Atiku da makamanciyar wannan bukatar.

To sai dai mako guda bayan bukatar shima zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya soki bukatar ta yan takarar PDP da LP.

Tuni dai kotun sauraran karar zaben tayi watsi da bukatun na yan takarar PDP da LP.

 

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...