Dakarun sojin ƙasar nan sun dawo da mazauna garin Mansur da ke karamar hukumar Alkeleri dake Jihar Bauchi gidajensu bayan sun yi gudun hijira sakamakon matsalar tsaro.
Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Mataimakiyar Daraktan Hulda da Jama’a ta Rundunar Sojin kasa ta 33 ta fitar a ranar Alhamis din data gabata 23 ga Afrilu.
Sanarwar ta bayyana cewa mazauna garin, sun bar gidajensu tun ranar 26 ga Fabrairu 2026 bayan hare-hare da suka tilasta musu yin gudun hijira, kafin a dawo da su bayan kammala ayyukan tsaro a yankin.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa an mika yankunan da aka kwato ga hukumomin tsaro da sauran hukumomi domin kula dasu tare da bai wa al’umma damar komawa gidajensu.
