Majalisar Dokokin Jigawa ta bada umarnin fara bincikar tsohuwar Gwamnatin Muhammad Badaru Abubakar.
Matakin ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar, wanda ya gudanar da cikakken bincike kan abunda ya shafi kudadan ma’aikatu.
Da yake gabatar da rahoton a zaman majalisar, shugaban kwamitin, Isyaku Abubakar, ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga rahotannin ofisoshin Babban Mai Binciken Kudi na Jiha da kuma na ƙananan Hukumomi, tare da gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a da kuma halartar manyan jami’an gwamnati.
Ya ce, an gayyaci kwamishinoni, manyan sakatarori da daraktocin kuɗi da kuma shugabannin ƙananan hukumomi domin yin ƙarin bayani kan wasu kuɗi, inda kwamitin ya tabbatar da bin ƙa’idoji a duk tsawon aikin.
Rahoton ya bayyana cewa, wasu matsaloli da suka haɗa da rashin cikakkun takardu, saɓani a bayanan kashe kuɗi, da kuma rauni kan tsarin sa’ido a matakin jiha da kuma ƙananan hukumomi.
