Tsohon dan takarar shugaba ƙasa a jam’iyyar LP a 2023 Peter Obi, ya jagoranci wata bababr tawaga ta ƴan siyasar kudu maso Gabas, domin ƙulla ƙawance da arewa maso gabas da sauran sassan Najeriya da manufar ciyar da ƙasar nan gaba.
Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din data gabata a Bauchi, bayan wata ganawa ta sirri da ya yi da gwamnan jihar ta Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad da masu ruwa da tsaki dangane da ƙullar siyasa mai dore wa.
Tsohon dan takarar shugaba ƙasar yana zagaye a faɗin ƙasar nan domin ƙulla ƙawance a dai dai lokacin da ake tunkarar babbar zaban kasar nan na shekrar 2027.
A makon da ya gabata ne dai magoya bayan Peter Obi dana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, suka kafa wata ƙungiya mai suna OK movement da ke son goyon baya ga takarar Obi da Kwankwaso a matsayin dan takarar shugaban kasa shugaba da kuma mataimaki a jam’iyyar ADC.
