
Aminu Abdullahi Ibrahim
World Peace Movement ta ƙaddamar da rangadi a Afirka na shekarar 2026
Rangadin na a matsayin wani babban shiri na yaɗa zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a faɗin nahiyar Afirka da ma sauran sassan duniya.
A jawabin da ya gabatar a nan Kano wanda ya assasa ƙungiyar, Sheikh Ahmad Dabbagh, ya bayyana cewa burinsu shi ne su isa dukkan ƙasashe 195 na duniya da saƙon zaman lafiya, da fahimtar juna ba tare da la’akari da bambancin addini, ƙasa ko asali ba.
An kama mutane sama da 1,000 bisa laifin hakar ma’adanai a Africa ta Kudu
Ya ƙara da cewa, zuwa yanzu ƙungiyar ta kai saƙonta zuwa sama da ƙasashe 70, bisa tsari da dabarun da aka shimfiɗa tun farko.

A cewarsa, manufar ba ta taƙaita ga kasashen musulmi ba. Ya ce manufar su itace isa ga duk inda mutane suke rayuwa, ko musulmi ko waɗanda ba musulmi ba.
Dalibai 135 masu lalurar gani ne suka rubuta jarrabawar JAMB a jihar Kano
Sheikh Dabbagh ya jaddada cewa wannan tafiya ta samo asali ne daga koyarwar Annabi Muhammad (SAW), wadda ta ginu a kan zaman lafiya, girmama juna da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ya ce nasara ta gaskiya ba ta ta’allaka ga tarin dukiya ko faɗaɗa iko ba, sai dai fifita mutuncin ɗan Adam fiye da komai.
Gwamnatin Tarayya da bankin musulunci sun kafa makarantar koyar da harsuna a Kano
Ahmad Dabbagh ya jagoranci hudumar sallar Juma’a a masallacin Isyaka Rabi’u dake Gauron Dutse tare da yin taro kan muhimmanci zaman lafiya a jami’ar Khairun dake Gadon Kaya.
Tarom ya samu halartar manyan Malamai Masana da dalibai daga sassa daban daban.
