Sabon ministan gidaje na kasa Dakta Muttaqha Rabe Darma ya ce nan da watanni uku za a gani sauyi a ma’aikatar gidaje.
Ya bayyana hakan jim kadan bayan da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya jagoranci rantsar dashi a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar shugaban ƙasar da ke birnin tarayyar Abuja.
Dakta Rabe Darma ya ce zai yi amfani da kwarewar da yake da ita wajan kawo sauye-sauye mai inganci a ma’aikatar gidaje ta kasa.
Sabon karamar ministan gidajen ɗan asalin jihar Katsina ne, ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa, wanda ya yi murabus a baya-bayan nan.
Dakta Muttaqha Rabe Darma ya kasance tsohon kwamishinan ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma sufuri na jihar Katsina, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan raya karkara a jihar ta
Sabon karamar ministan gidajen na kasa ya riƙe muƙamai daban-daban a baya da suka haɗa da babban sakataren asusun fasahar man fetur daga 2008 zuwa 2012
