Cutar zazzabin Lassa ta yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya a Jihar Oyo, yayin da gwamnati ta tabbatar da samun mutum biyar da suka kamu da cutar a wasu yankuna.
Kwamishinar Lafiya ta jihar, ta bayyana cewa an ɗauki matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar.
Ta ce ana kula da waɗanda suka kamu da cutar a cibiyoyin killace marasa lafiya, ciki har da cibiyar cututtuka masu yaɗuwa da kuma asibitin koyarwa na jihar.
Ta ƙara da cewa an ƙarfafa sa ido, inda sama da mutum 200 ake bibiyar su, tare da shirya magunguna da sauran kayan aiki. Haka kuma ana ci gaba da tsaftar muhalli, feshi, da wayar da kan jama’a.
Tuni dai gwamnan jihar, Seyi Makinde, ya amunce da fitar da kuɗaɗen wadanda zasu taimaka wajan ɗaukar matakan kariya.
