Tsohon ministan harkokin wajan kasar nan Ambasada Yusuf Maitama Tugga ya bada tabbacin magance matsalar yawan yaran da basa zuwa makaranta a jihar Bauchi.
Ambasada Yusuf Tugga na wannan jawabin ne a lokacin da yake jawabi a hedikwatar jami’iyyar APC ta jihar Bauchi tare da bayyana anyyar sa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Buachi a shekarar 2027.
Tsohon ministan harkokin wajan ya sake yin kira ga ‘yayan jami’iyyar APC dasu hada kan su wajen gudu domin samun nasarar jami’iyyar.
Ambasada Yusuf Maitama Tugga ya tabbatar da cewa, zai goyi bayan duk wanda ya samu nasara a matsayin dan takarar gwamna a jihar Bauchi domin ciyar da jihar gaba
