Masu sha’awar tsayawa takara a zaben 2027 sun fara nuna shaawarsu, ta son tsayawa takara ta hanayar fitowa tare da bayyanawa duniya burinsu na ganin sun rabauta da takara a zaben.
Wannan na zuwa ne bayan da jamiyyar APC matakin kasa ta tabbatar da cew,a babu wani dan majalisa da yake da damar takara ta kai tsaye, ko da kuwa yana kan kujerar sai dole jamiyyar da yake ciki ta gudanar da taron raba gardama tsakaninsa da wadanda ke shaawar wannan kujera.
