Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDalibai 'yan asalin Kano dake karatu a jami'ar tarayya dake Dutse a...

Dalibai ‘yan asalin Kano dake karatu a jami’ar tarayya dake Dutse a Jigawa sun roki gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya biya musu kudin makaranta

Date:

Dalibai ‘yan asalin jihar Kano dake karatu a Jami’ar tarayya dake Dutsen jihar Jigawa sunyi kira ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya kai musu dauki ta hanyar tallafasu da kudin makaranta.

Mai magana da yawun shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kano dake karatu a Jami’ar ta F.U.D Ibrahim Yunusa, ya ce da yawan daliban sun biya kaso 60 na kudin makarantar a zangon karatu na farko inda suke neman gwamna Abba Kabir Yusuf, da ya tallafa ya biya musu kaso 40 na zangon karatu na biyu da za a fara a wannan mako.

Ya ce akwai kusan dalibai dubu bakwai a jami’ar ‘yan asalin jihar Kano da zasu iya barin karatu saboda kudin makaranta duk da suna dab da gamawa.

Ibrahim Yunusa ya kara da cewa daliban dake karatu a jami’ar tarayya ta Dutse ‘yan asalin jihar Kano sun fi bukatar daukin gwamnan kasancewar suna nesa da gida.

“makaranta ta baiwa dalibai damar biyan kudin kowane zangon karatu maimakon biya a dunkule.

To mun biya na zangon farko kaso sittin yanzu na zango na biyu zamu biya wanda shine kaso arba’in,” a cewar sa.

Kungiyar daliban ‘yan asalin jihar Kano dake karatu a Dutsen jihar Jigawa ta bukaci gwamnan da ya duba koken su domin kai musu dauki duba da cewa da yawa zasu iya ajiye karatun su.

Kaso 60 na dalibai ne suka ci jarrabawa a bana-NECO
Idan za a iya tunawa a makonin da suka gabata ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf, ya dauki nauyin biyawa dalibai ‘yan asalin jihar Kano dake karatun digirin farko kudin makaranta na Jami’ar Bayero.

Latest stories

Related stories