Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga ƴan jam’iyyar APC da su fita su kaɗa ƙuri’a a zaɓen fitar da ‘ƴan takarar da za su wakilci jam’iyyar a babban zaɓen ƙasar, inda ya buƙace su da su gudanar da zaɓen cikin lumana.
A gobe Juma’a ne za’a fara gudanar da zaɓen fitar da ‘ƴan takarar APC, inda za a fara da zaɓen fitar da ‘ƴan takarar majalisar wakilai.
Ya ce zaɓe na cikin manyan ginshiƙan dimokuraɗiyya, sannan ya yi kira da a gudanar da zaɓen fitar da ‘ƴan takarar a matsayin ‘ƴan uwa.
Tinubu ya kuma yi kira ga waɗanda ba su yi nasara ba da su yi haƙuri su raka waɗanda suka yi nasarar, domin a cewarsa, wanda ya yi nasara shi ne wanda ya yi haƙuri ya jira wani lokaci, ba wanda zai fasa kowa ya rasa ba.”
Shugaban ya kuma ce waɗanda suka yi nasara ya kamata su ja kowa a jiki.
