Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAisha Buhari Ta Mika Bayanan Barin Mulki Ga Matar Tinubi.

Aisha Buhari Ta Mika Bayanan Barin Mulki Ga Matar Tinubi.

Date:

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce ofishinta ya mika wasu takardu ga uwargidan shugaban kasa mai jiran rantsuwa, Oluremi Tinubu.

Da take magana a fadar shugaban kasa a Larabar nan, Uwargidan shugaban kasar mai barin gado ta bayyana cewa takardun za su zama nuni ga nasarar ofishinata.

Aisha ta kuma mikawa Madam Oluremi tambarin tawagar zaman lafiya ta matan shugabannin Afirka, kasancewarta babbar mai masaukin baki ga dukkan matan shugabannin kasashen Afirka.

A martanin ta, Madam Oluremi ta bayyana godiyarta ga Aisha Buhari, in da bayyana ta a matsayin Abar kwaikwayo babba ta fuskar jagoranci, tare da yaba mata kan yadda ta gudanar da ayyukanta.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, wannan shine karo na farko a hukumance aka mika mulki a ofishin uwargidan shugaban kasar.

Latest stories

Related stories