Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKimanin mutum miliyan biyar zasu halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnatin Kano

Kimanin mutum miliyan biyar zasu halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnatin Kano

Date:

Kimanin mutane miliyan 5 ne ake hasashen zasu halarci bikin rantsar da sabuwar gwamnati a jihar Kano.

Shugaban kwamatin kula da harabar taron, Mallam Kabiru Gwarzo ne ya bayyana hakan, a zantawar da nayi da shi.

Yace ana tsammanin halartar baki daga sassan daban daban na Najeriya har ma da makobta, kasancewar jihar Kano cibiyar magoya bay Kwankwasiyya.

Litinin mai zuwa, 29 ga watan da muke ciki ne gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusif zai sha rantsuwar kama aiki, bikin da zai wakana a filin wasa na Sani Abacha dake nan Kano.

Kimanin bandakunan tafi da gidanka 200 ne za a samar a filin wasan na Sani Abacha.

A cewar Mallam Kabiru Gwarzo, an shirya hakan ne domin saukakawa mahalarta taron biyan bukatun su, tare da tabbatar da tsaftar wurin.

Latest stories

Related stories