Saurari premier Radio
26.3 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai"Ba zamu yarda ministoci su mallake motocin ofis ba" - fadar Shugaban...

“Ba zamu yarda ministoci su mallake motocin ofis ba” – fadar Shugaban kasa

Date:

Fadar shugaban kasa tace babu guda cikin ministocin gwamnati mai barin gado da za a bari ya mallake motocin aikin ofis bayan mika mulki.

Tace za a bar su ne kadai da abinda doka ta tabbatar a matsayin rabon su.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan, a zantawarsa da jaridar Punch.

Yace hatta shugaba Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, zasu bar motocin su na alfarma ne ga magadansu.

Rahotanni sun ce bisa al’ada, masu rike da mukaman siyasa kan mallake ababen hawar gwamnati bayan sauka daga mulki, yayinda wadansu ke karya farashin su, tare da siyawa kai.

Garba Shehu yace tuntuni, akwai dokar da ta amincewa baiwa tsaffin shugabanni wani adadi na ababen hawa bisa kayyadajjen zango, kuma shima shugaba Buhari, ba zai ketare hakan ba.

An kiyasta farashin mota mai silke da shugaban da mataimakinsa suka hau, kirar Marcedese Benz akan kudi naira miliyan 300.

A shekarar 2018, an ware kimanin naira miliyan 907 domin sayen sabbin motocin da kuma wasu kayan kula da jirgin shugaban kasa.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...