Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJirgin Farko Na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya.

Jirgin Farko Na Maniyyatan Jihar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya.

Date:

Jirgin farko na maniyyatan jihar Jigawa ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Jirgin na kamfanin Max Air kirar Boeing 747 da ya taso daga filin jirgin saman Dutse da ke jihar Jigawa, ya dakatar da tafiya zuwa kasar Saudiyya a lokacin da ya samu da matsalar.

Wata maniyyaciyya da ta ce suna zaune a cikin jirgi ana kokarin sauya musu wani jirgin don ci gaba da tafiya.

A cewarta, matsalar ta afku ne sakamakon kankarar ruwan sama da ta bugi gilashin jirgin lamarin da ya janyo tsagewarsa.

Hakan dai ya tilastawa jirgin fasa tafiya kasar ta Saudiyya tare da juyowa nan Kano.

Kawo yanzu dai babu wani jami’i da ya magantu kan hakan.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...