Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnonin arewa ta tsakiya sun bukaci a basu mataimakin shugaban majalisar dattawa

Gwamnonin arewa ta tsakiya sun bukaci a basu mataimakin shugaban majalisar dattawa

Date:

Gwamnonin yankin Arewa ta tsakiya sun bukaci uwar jam’iyyar APC ta kasa da zababben shugaban kasa Bola Tinubu su sake duba kunshin shugabancin majalisa ta goma da suka  fitar.

Gwamnonin sun bukacin hakan ne bayan wata ganawar masu ruwa da tsaki na shiyar, wanda suka gudanar da babban birnin tarayya Abuja.

Gwanmonin sun ce zasu gana da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu don sanar da shi matsayar su na kin amincewa da yadda aka raba shugabancin majalisa ta goma.

Tunda fari dai  zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana goyon bayan sa  ga Sanata Godswill Akpabio daga yankin kudu maso kudu a matsayin dan takarar shugabancin majalisar dattawa, sai kuma  Sanata Barau Jibril daga yankin Arewa maso yamma a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.

A yayin da a majalisar wakilai, jam’iyyar ta tsaida Tajudeen Abbas daga yankin Arewa maso Yamma a matsayin kakakin majalisar da kuma Benjamin Kalu daga yankin kudu maso gabas a matsayin mataimakinsa.

Hakan ya sanya gwamnonin Arewa maso tsakiya suka ce ba a yi musu adalci ba, inda suka bukaci a bawa yankin dama ya kawo mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Gwamnonin da suka halarci tattaunawar sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya kuma gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Plateau Simon Lalong, gwamnan Kwara Abdulrahaman Abdulrazaq, Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, sai  Yahaya Bello na jihar Kogi.

Sauran mahalarta taron sune zababben gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia, da dan takarar shugabancin majalisar dattawa Sanata Mohammed Sani Musa, sai mataimakin shugaban majalisar wakilai  Ahmed Idris Wase da sauransu.

Tuni dai shugaban jam’iyyar APC  na kasa Abdullahi Adamu ya sanar da cewa zasu sake yin nazari kan wannan, bayan kiraye-kiraye da nuna kin amincewa da ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar.

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...