Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya samar da guraben aiki miliyan 12-Garba Shehu

Buhari ya samar da guraben aiki miliyan 12-Garba Shehu

Date:

Mai Magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samar da guraben aiki miliyan sha biyu a bangaren noma cikin shekaru takwas.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne a cikin shirin safe na gidan talabijin na Channels, yana mai bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta yi namijin kokari  a bangaren samar da tsaro, wutar lantarki har ma da yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa a bangaren noma kadai, Kungiyar manoman shinkafa ta kasa ta samar da sabbin guraben ayyukan yi fiye da miliyan sha biyu, inda ya ce gwamnatin Buhari ta gaji kamfanin takin zamani guda hudu daga gwamnatin da ta shude, wanda yanzu haka ake da guda hamsin da biyar da suke aiki ba dare ba rana.

Yanzu haka tattalin arzikin kasar nan ya dena dogara da man fetur, inda bangaren noma ke jan ragamar tattalilin arzikin kasar, kuma Najeriya tana samar da abincin da zata ci.

A bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa, Garba Shehu ya ce shugaban Muhammadu Buhari bashi da wani asusun banki da yake boyen kudaden sata, don hakan baya tsoron bincike bayan ya bar mulki.

Latest stories

Related stories