Ƴan sandan Jamus sun kama ƴan Najeriya 11 da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne da suke shirya soyayyar ƙarya don yaudara.
A wata sanarwa da ƴan sandan Bavarian suka fitar, ƴan ƙungiyar asirin ta Black Axe sun aikata manyan laifuka da dama a faɗin duniya.
Ƴan sandan sun ƙara da cewa ƙungiyar ta mayar da hankali kan ƙulla soyayyar ƙarya da kuma halasta kuɗin haram a Jamus.
Sanarwar ta ce, suna yin ɓadda kama, misali suna zuwa da niyyar aure sannan bayan an ɗau wani lokaci ana soyayyar sai su nemi a basu kuɗaɗen yin wasu ɓukatu.
Ɓangarorin da ƙungiyar take aiki a faɗin duniya sun haɗa da safarar bil’adama da yaudara da halasta kuɗin haram da safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka kama ɗin duka ƴan Najeriya ne kuma ƴan shekaru tsakanin 29 da 53.
An tsare su a ranar Talata a sumamen da aka kai yankin Bavaria bayan binciken ƴan sanda da aka shafe sama da shekara biyu ana yi.