Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumi"Bazamu karbi kasa da Dubu 350 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba"...

“Bazamu karbi kasa da Dubu 350 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba” Kungiyar Ma’aikatan Jami’a a ta ƙasa NAAT.

Date:

Kungiyar Ma’aikatan Jami’a ta kasa NAAT ta sha alwashin cewa ba za su karbi kasa da naira dubu 350 ba a matsayin mafi karancin albashi, lura da tsadar kayan masarufi, sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin kasar nan ta yi.

Shugaban kungiyar, Kwamred Ibeji Nwokoma, ya ce ya zama wajibi mafi karancin albashi ya zama wanda zai iya rike ma’aikaci da masu dogaro da shi, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa.

Kwamared Ibeji ya fadi hakan ne a lokacin taron deliget din kungiyar na kasaa karo na 5 a jami’ar Abuja.

Yace Wasu kasashen Afirka sun dauki kwararan matakai wajen tabbatar da cewa albashin ma’aikaci zai iya ba shi damar samun yin rayuwa cikin rufin asiri da wadata.

Game da bashin albashin da ma’aikatan jami’a ke bin gwamnati kuwa, Kwamred Nwokoma ya ce wannan babban abin takaici ne saboda ya kara jefa su cikin matsi tare da kashe masu kwarin gwiwar yin aiki.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...