Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFursinoni 118 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja dake Jihar Neja.

Fursinoni 118 ne suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja dake Jihar Neja.

Date:

Akalla fursunoni 118 sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren Laraba.

Jaridar daily trust ta bayyana cewa fursunoni da adadinsu ya kai 118 sun yi amfani da damar ruwan sama wajen tserewa.

Ruwan saman da ya mamaye ko’ina a cikin garuruwan Neja da ma makwaftakan garuruwan birnin tarayya Abuja ya lalata wasu sassan katangar gidan yarin.

Wani mazaunin garin Abdullahi Nura ya shaida wa manema labarai cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke bakin aiki inda suka tsere ta bangarori daban-daban.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin fursunonin sun yi amfani da duwatsu wajen tarwatsa mutanen da suka kawo agaji domin hana su tserewa.

A halin yanzu an baza tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa cikin garin Suleja domin kamo fursunonin da suka tsere.

Wani mazaunin garin Suleja, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Gaskiya ne lamarin ya faru kuma sun taimaka wajen kamo biyu daga cikin fursunonin, kuma sun mika su ga hukumar gidan yarin.

An kuma tattaro cewa jami’an tsaro na ta harbe-harbe a saman iska domin tsoratar da fursunonin da suka tsere su fito daga maboyarsu.

Channels TV ta ruwaito cewa an dan samu nutsuwa yanzu yayin da mutane suka ci gaba da gudanar da al’amuran su na yau da kullum yayin da ake ci gaba da neman fursunonin.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...