Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDA DUMI-DUMI: Tinubu ya gana da Kwankwaso a kasar Faransa

DA DUMI-DUMI: Tinubu ya gana da Kwankwaso a kasar Faransa

Date:

Rahotanni na bayyana cewa zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa.

Tinubu da Kwankwaso sun yi ganawar ne a litinin din da ta gabata Paris, babban birnin kasar Faransa, inda suka shafe awanni suna tattauna, wadda ke da alaka da samar da hadin kai don nufin yin aiki tare, inda Tinubu ya bukaci Kwankwaso ya sanar da abokan siyasarsa cewa yana neman hadin kansu domin su yi aiki tare.

An ruwaito cewa Kwankwaso ya samu rakiyar mai dakinsa Hajia Salamatu da kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji Abdulmimin Jibrin, yayin da Tinubu ke tare da mai dakinsa Sanata Oluremi Tinubu da kakakin majalisar wakilai mai baring ado Femi Gbajabiamila.

Tinubu da Kwankwaso sun amince su kara haduwa a nan gaba domin kara yin wata tattaunawar.

Latest stories

Related stories