Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKano: Masu garkuwa da mutane sun hallaka dan uwansu yayin da suke...

Kano: Masu garkuwa da mutane sun hallaka dan uwansu yayin da suke shirin sace mutane

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan bindiga uku da suka yi yunkurin yin garkuwa da wani uba da dansa a kauyen Yarimawa da ke karamar hukumar Tofa.

Lamarin ya faru ne bayan da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan wani Nasiru Yahaya tare da yunkurin yin garkuwa da shi da dansa Gaddafi Nasiru, amma dan ya yi turjiya, lamarin da ya kai ga fada.

Yayin da suke kokarin harbe yaron, masu garkuwa da mutanen sun harbe daya daga cikinsu wanda ya mutu nan take.

Da yake gabatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan Kano, Muhammed Usaini Gumel, ya ce, “An samu rahoton cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan wani Nasiru Yahaya da ke kauyen Yarimawa a karamar hukumar Tofa a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da shi da dansa.

Da suke amsa laifin, wadanda ake zargin sun ce sun samu labari daga wani dan cikin gida wanda ya ce su je gidan su yi garkuwa da mahaifin da dansa.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce, “Mun je gidan kamar yadda aka umarce mu. Amma dan ya yi turjiya, yayin da muke harbe shi, mun harbe dan kungiyarmu. Ban taba yi ba; wannan ne karo na farko kuma na yi nadamar yin hakan.”

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...