Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu a Kano ta aike da wani matashi gidan gyaran hali da...

Kotu a Kano ta aike da wani matashi gidan gyaran hali da tarbiya bisa zargin hallaka mahaifiyarsa

Date:

Wata kotun Majistare a nan Kano ta aike da matashin da ake zargi da hallaka mahaifiyarshi zuwa gidan yari.

Matashin dan shekaru 22 ana zarginshi da da laifin kisan mahaifiyarsa ’yar kimanin shekaru 50 da haihuwa ta hanyar caka mata wuka.

Tun da farko mai gabatar da kara Barista Rabia Saad ta shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya caccakawa mahaifiyarshi wuka a sassan jikinta, kuma hakan yasa aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed inda likita ya tabbatar da cewa ta rasu.

Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa, laifin dai ya saba da sashe na 221 na Kundin Shari’ar Pinal Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Kofar Mata ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari kafin adawo zaman kotun 27 ga watan Yuni mai zuwa.

Latest stories

Related stories