Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaAkalla mutane 40,000 ke rasa rayukan su sakamakon hadura a shekara -FRSC

Akalla mutane 40,000 ke rasa rayukan su sakamakon hadura a shekara -FRSC

Date:

 

Hukumar kiyaye afkuwa haddura ta kasa FRSC, ta ce fiye da mutane dubu arba’ in ne ke rasa rayukansu a duk shekara sakamakon hadarin ababen hawa a fadin kasar nan.

Shugaban hukumar na kasa, Dauda Biu ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bukukuwan tunawa da wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hadarin mota wanda majalisar dinkin duniya ta ware mako guda  domin tunawa da su.

Dauda Biu ya ce wannan bayanai na daga cikin munanan kididdigar da hukumar ta samu na haduran ababen hawa wanda ke haddasa mutuwa ko nakasa.

Ya kara da cewa mutane miliyan daya da dubu dari uku ke rasa rayukansu a dalilin haduran ababen hawa, yayin da akalla mutane  miliyan 50 ke samun raunuka a duk shekara a fadin duniya.

Shugaban hukumar ya kuma ce majalisar dinkin duniya ta samar da wani tsari na kiyaye afkuwar haddura na shekaru goma daga 2021 zuwa 2030, wanda hakan gagarumar nasara ce na rage yawan mace-macen da al’umma keyi yayin afkuwar hadarin.

Abdullahi Aliyu Labaran, shine jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye  haddura na kasa reshen jihar kano, ya ce an samu raguwar haduran sakamakon taron bitar da hukumar kiyayen haduran keyi ga kungiyar direbobi.

 

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...