Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar kashe gobara ta kubutar da wani matashi da ya fada rijiya

Hukumar kashe gobara ta kubutar da wani matashi da ya fada rijiya

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta kubutar da wani matashi mai suna Bashir Muhammad, daga cikin wata rijiya a unguwar Dandago Bola.

Haka zalika hukumar ta kubutar da wasu karin mutane uku ýan uwan matashin da sukayi kokarin fito da shi daga rijiyar.

Mai Magana da yawun hukumar nan Kano Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace sun sami kiran gaggawa ne daga wata mata mai suna Umma Usman Dandago, inda ta sanar da su afkuwar al’ámarin.

Ya kara da cewa, bayan samun rahoton ne jami’ánsu suka isa unguwar kuma suka yi nasarar ceto matashin, wanda ya samu karaya a kafa da hannu kamar yadda ya shaida.

Hukumar ta yi gargadi ga al’ummar jihar da su yi taka tsantsan don gudun faruwar irin wannan al’amari, inda ta yi kira a ringa sanar da su faruwar ibtila’I cikin gaggawa.

Latest stories

Related stories