Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZamu ci gaba da neman man fetur a tafkin Chadi-NNPC

Zamu ci gaba da neman man fetur a tafkin Chadi-NNPC

Date:

Shugaban Kamfanin man fetur na kasa NNPC Malam Mele Kyari ya ce a sati mai zuwa zasu ci gaba da neman man fetur a yankin tafkin Chadi.

Malam Mele Kyari ya bayyana hakan a litinin din data gabata, yayin da ya jagoranci shugabannin kamfanin zuwa shelkwatar kamfanin Media Trust mamallakan jaridar Daily Trust, gidan talabijin na Trust da kuma Radiyo Trust dake babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ci gaba da hakar man fetur a wani bangare na tafkin Chadi dake jihar Borno, bayan dakatar da aikin shekaru biyar da suka gabata sakamakon rikicin ‘yan tada kayar baya a yankin arewa maso gabas.

Shugaban na NNPC ya kara da cewa samun mai a kogin Kolmani dake tsakanin jihar Gombe da Bauchi a watan nuwamban shekarar data gabata ya kara musu karsashi wajen zage damtse na ci gaba da neman man fetur a tafkin na Chadi.

A cewar Kyari samun mai a Kolmani ya taimaka musu wajen kara gano wasu sassa da man yake a jihar Nasarawa, a don haka ne zasu ci gaba da aikin a sati mai zuwa.

 

Latest stories

Related stories