Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSabuwar gwamnati:Tinubu zai fara ziyarar aiki: |Premier Radio| 10.05.2023

Sabuwar gwamnati:Tinubu zai fara ziyarar aiki: |Premier Radio| 10.05.2023

Date:

Zababban shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci nahiyar turai domin fara ziyarar aiki daga ranar Laraba.

Ofishin zababbeen shugaban kasa ne ya fitar da sanarwar cewa Tinubu zai yi amfani da tafiyar domin lura da shirye-shiryen mika mulki da kuma tsare-tsarensa.

Gabanin tafiyar tasa, Tinubu ya gana da Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu wadanda jam’iyyar APC ke mara wa baya domin zama Shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa.

Ana saran dai Tinubu zai dawo Najeriya gabanin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watn Mayu.

Latest stories

Related stories