Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYa kamata mu tashi tsaye domin kawo karshen rikicin Sudan-Aisha Buhari |...

Ya kamata mu tashi tsaye domin kawo karshen rikicin Sudan-Aisha Buhari | Premier Radio | 10.05.2023

Date:

Uwargidan Shugaban kasa, Aisha Buhari ta roki a hada karfi da karfe don ganin an kawo karshen rikicin da ke wakana a kasar Sudan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Aisha Buhari na wannan kira a wani taro da ta jagoranta a makon da muke ciki a Fadar Gwamnati da ke Abuja.

A cewar jaridar, Aisha Buhari na ganin akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji Sudan.

Tun ranar 15 ga watan Afrilu, yaki ya barke a Sudan kuma har wannan lokaci, an kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Sama da mutane 500 ake kyautata zaton cewa rikicin ya yi sanadin rasuwarsu kawo yanzu.

Latest stories

Related stories