Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYANZU-YANZU: Kotun koli ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun

YANZU-YANZU: Kotun koli ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun

Date:

Kotun koli ta tabbatar da Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Mai shari’a Emmanuel Agim, wanda ya karanta hukuncin a ranar Talata nan, ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara, wadda ta tabbatar da nasarar zaben Ademola Adeleke.

Kwamitin alkalai mai mutune biyar na kotun koli, ya ce kotun daukaka kara da ta tabbatar da Adeleke a matsayin gwamna daidai ne.

Tunda fari dai, Oyetola da jam’iyyar sa ta APC sun garzaya kotun koli ne, inda suka roki kotun da ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke wanda ya karyata hukuncin da kotun baya da ta yanke.

Idan za a iya tunawa kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Osun, wadda ta mayar da Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2022.

Latest stories

Related stories