Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKano: ‘Yan sanda sun kama masu kwacen waya 83 a yayin bukukuwan...

Kano: ‘Yan sanda sun kama masu kwacen waya 83 a yayin bukukuwan karamar sallah

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama masu kwacen waya da yan daba su 83 dauke da muggan makamai a lokutan da aka bukukuwan karamar sallar bana.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Larabar nan.

Ya ce an kama wasu daga cikin su da muggan makamai, ya yin da wasu kuma suka fito domin yiwa jama’a fashi da kuma ji musu raunuka.

Kiyawa ya kara da cewa sun samu nasarar kama dilolin kwaya da kuma masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, wadanda dukkaninsu an same su da kayayyakin da ake zarginsu da aikata laifuka.

Ya kara da cewa sun kama wani mai suna Usman Saleh Gwarzo da ake zargi da yin amfani da itace wajen kwacen Baburan Mutane, wanda bayan kama shi rundunar ta gano cewa sanye yake da Hijabin mata ajikinshi.

Sai dai mai lafin ya ce a al’adarsu ta Fulani ba sai mata ne kadai suke sanya Hijabi ba harda Maza.

Rundunar yan sandan Kanon ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaron al’umma, tare da gargadin masu aikata laifi da kuma jan hankalin mutane da su cigaba da yi wa jihar Kano addu’a.

Latest stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...

Related stories

Gwamnan Katsina ya nemi tallafi kan karancin abinci da matsalar tsaro ta haddasa.

A wani alk’amarin kuma, Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda,...