Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban daliban Yusuf Maitama Sule ya bukaci a kara adadin sabbin daliban...

Shugaban daliban Yusuf Maitama Sule ya bukaci a kara adadin sabbin daliban da ake wa Gwajin lafiya

Date:

 

Tafida Akilu wanda shine sabon shugaban kungiyar dalibai na jami’ar ta Yusuf Maitama Sule dake nan a jihar kano yayi  kira da a kara adadin sabbin daliban da ake duba lafiyar su a asibitin jamiar dake mazaunin ta na dindin a Kabuga.

 

Tafida yayi wannan kira ne a yayin wani rangadi da yayi a safiyar yau laraba  domin ganin yadda duba lafiyar daliban yake gudana.

 

Wannann duba lafiyar ana yin sa ne ga dukkanin sababbin daliban da aka bawa gurbin karatu a jami’ar, domin tabbatar da cikakkiyar lafiya kafin fara karatu.

 

A yayin ziyarar tasa Tafida ya tattauna da Jami’an hukumar lafiya na jami’ar dake cikin makarantar domin ganin an kara adadin daliban da ake dubawa a rana domin ganin an saukakawa daliban wahalar azumi.

 

A karshe shugaban daliban yayi kira da sabbin daliban da su dena cinkushewa a can sashin na Kabuga da suke zuwa daya sashin dake kofar Nasarawa.

 

 

Latest stories

Related stories