Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta karbi kararrakin zabe takwas a jihar Kebbi

Kotu ta karbi kararrakin zabe takwas a jihar Kebbi

Date:

Kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Kebbi ta karbi karofe korafen zabe takwas na zaben majalisun dokoki na tarayya da aka kammala.

Sakataren kotun Abdulraham Muhammad, ne ya bayyana haka yayin ganawar sa da manema labarai a birnin Kebbi.

Ya ce shida daga cikin korafin na zaben majalisar wakilai ne yayin biyu kuma suka kasance na majalisar dattijai.

Ya ce Sanata Bala Ibn Na’Allah, na APC ya shigar da korafi da yake kalubalantar nasarar da dan takarar PDP Garba Musa, yayi akan sa a zaben sanatan Kebbi ta kudu.

Shima gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu, na APC ya shigar da korafi inda yake kalubalantar nasarar da Muhammad Adamu Aliero na PDP ya samu a zaben sanatan Kebbi ta tsakiya.

Sakataren kotun sauraran korafe korafen zaben ya kuma ce dan takarar majalisar wakilai na APC Farfesa Mukhtar Umar Bunza ya kalubalanci sakamakon zaben majalisar wakilai na birinin Kebbi da Kalgo da kuma Bunza.

Sai Muhd Bala Usman na PDP dake kalubanalantar sakamakon zaben Yauri da shanga da kuma Ngaski.

Inda shima Muhd Umar Jega, ya ke kalubalantar zaben yankin Gwandu da Jega da Aliero.

Sai Bello Kabiru da ya shigar da korafi yana kalubalantar zaben dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Suru da Bagudo.

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zabe

Abdulraham Muhammad, ya ce ‘yan takara suna da kwanki 21 ne kawai daga sanda aka sanar da sakamakon zabe don gabatar da korafin su a kotun sauraron kararrakin zabe.

Ya kuma ce kotun zata sanar da lokacin fara sauraron korafe korafen zaben da Zarar ta gama tattara su daga dukkan jam’iyun.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...