Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBamu yarda da sakamakon gwamnan Kano ba-APC

Bamu yarda da sakamakon gwamnan Kano ba-APC

Date:

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC mako daya ta sake nazari kan sakamakon zaben gwamna na jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris.

jam’iyyar APC Kano ta ce bata yarda da sakamakon zaben gwamnan Kano da ya bayyana Abba Kabir na jam’iyyar NNPP  a matsayin wanda ya lashe shi ba.

jam’iyyar ta bayyana haka ne ta bakin lauyantaBarista Abdul Fagge a taron manema labaran da ta gudanar ranar Talata.

APC ta ce baturen zaben ya yi kuskuren fahimtar dokar zabe wajen banbance soke sakamakon wasu wurare da aka yi sanadin tashin hankali da kuma zabe fiye da kima.

APC dai ta ce sam ba ta yadda da hanyar da aka bi wajen sanar da sakamakon zaben ba har aka bayyana Abba Kabir a matsayin zababben gwamna a don haka ta nemi a gaggauta sake yin zagaye na biyu na zaben.

Sai dai a cewar lauyan, baturen zaben ya yi la’akari ne kawai da batun tashin hankali wajen kare tazarar da ke tsakanin yan takara biyu – Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasir Gawuna na APC

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...