Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNa Kagu na bar mulkin Najeriya-Buhari

Na Kagu na bar mulkin Najeriya-Buhari

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya ƙagara ya sauƙa daga mulkin Najeriya, kamar yadda ya sha nunawa a baya cewa ya matsu ya ga ranar 29 ga watan Mayu domin ya miƙa mulki ga magajinsa.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ganawar ban-kwana da jakadiyar Amurka mai barin-gado, a Najeriya, Mary Beth Leonard, a fadar shugaban, da ke Abuja a yau Talata.

Buhari ya furta hakan ne yayin mayar da jawabi ga jakadiyar kan tambaya da ta yi masa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban shi ma mai barin-gado ya ƙara da cewa yana son ya koma ya mayar da hankalinsa kan kula da gonakinsa da kuma dabbobinsa sama da 300 a Daura idan ya sauƙa daga mulki.

Buhari, wanda ya nuna gamsuwa da irin sha’awar da ‘yan Najeriya suka nuna kan dumukuraɗiyya ta hanyar waɗanda suka zaɓa a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun dokoki na tarayya da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun dokoki na jihohi da aka kammala, ya ce lalle dumukuraɗiyyar ƙasar ta bunƙasa.

Ya ce mutane sun fahimci ƙarfi da ikon da suke da shi, waɗanda idan aka ba su damar zaɓe cikin walwala da adalci ba wanda zai gaya musu abin da za su yi.

”Na yi farin ciki da yadda wasu ƴan takara suka faɗi a zaɓen, ” in ji Buhari.

Ya ce sakamakon canjin kuɗi da gwamnatinsa ta yi ba a samu kuɗin da za a ba masu zaɓe ba, wanda kuma duk da hakan ma ya ce mutane su karɓi kuɗin amma su zaɓi wanda ya kwanta musu a rai, in ji shi.

Shugaban ya ce ya ji daɗi yadda bai yi katsa-landan a harkar zaɓen ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...