Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMuna cigaba da tattara bayanai game da gobarar kasuwar kurmi - SEMA

Muna cigaba da tattara bayanai game da gobarar kasuwar kurmi – SEMA

Date:


Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano ta ce tana cigaba da tattara alkaluma na shagunan da iftila’in gobara ya rutsa dasu a kasuwar Kurmi dake nan Kano.


Shugaban hukumar na Kano Dr Sale Jili ne ya bayyana haka a zantawarsa da Premier radio da safiyar Asabar din nan.


Ya kara da cewa kimanin sama da naira miliyan 140 akayi asara a gobarar hakan yasa suke tattara bayanai domin samarwa yan kasuwar tallafin daya dace.


A lahadin data gabata ne gobarar ta tashi a wannan kasuwa da tayi sanadiyyar konewar sama da shaguna 80 da asarar dumbin dukiyoyi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...