Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Kogi ya musanta rade-radin da ake cewa ya koma PDP.

Gwamnan Kogi ya musanta rade-radin da ake cewa ya koma PDP.

Date:

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin watsar da tafiyar Tinubu ya tsunduma rundunar Atiku.

 

Wasu rahotanni sunta zagayawa cewa gwamna Yahaya Bello na Kogi na shirin watsar da Tinubu ya koma tafiyar Atiku Abubakar na PDP.

 

Rahoton ya yi ikirarin cewa Mista Bello yana fargabar cewa Tinubu na iya marawa James Faleke baya a 2023 a takarar gwamnan jihar Kogi.

 

Sai dai kuma fadar gwamnatin Kogi ta fitar da sanarwar cewa babu wannan batu a tsarin gwamna Bello.

 

Darektan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa wannan labarin ƙanzon kurege.

 

Fanwo ya ce jihar Kogi ta APC ce kuma Tinubu ne kawai a gaban gwamnan jihar kuma shi yake wa aiki.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...