Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaShekaru 29 ba tare da mun samu kwararren likita a asibitin garin...

Shekaru 29 ba tare da mun samu kwararren likita a asibitin garin zakirai ba –Alumma

Date:

Al’ummar garin Zakirai da ke jihar Kano sun bayyana takaicinsu kan yadda su ka shafe shekaru 29 ba tare da gwamnati ta samar musu da babban likita a asibitin da aka gina tun lokacin mulkin gwamna Abdullahi Wase ba..

 

A shekarar 1994 ne gwamnatin jihar Kano ta gina asabitin na garin Zakirai kuma yana karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar sai dai har wannan lokaci babu babban likita a asibitin.

 

Garin Zakirai wanda shi ne hedikwatar ƙaramar hukumar Gabasawa na da nisan kilomita 42 daga birnin Kano kuma garin yana da yawan mutane fiye da dubu dari ɗaya, sai dai al’ummar wannan gari na fuskantar kalubale daban-daban musamman a ɓangaren kiwon lafiya.

 

Al’ummar garin sunce suna samun matsala musamman a lokacin da mata su ka zo haihuwa ko kuma wata larura da ta ke bukatar babban likita.

 

Baya ga rashin babban likita a asibitin kuma suna fama da rashin ma’aikata da za su iya bayar da tallafi ga kananan cututtuka.

 

 

 

Latest stories

Related stories