Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN ya zargi bankuna da yi masa zagon kasa

CBN ya zargi bankuna da yi masa zagon kasa

Date:

Babban Bankin kasa (CBN) ya zargi wasu bankuna da yi masa zangon kasa ta hanyar boye sabbin takardun kudade tare da ci gaba da bayar da tsofaffi.

 

Hakan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 10 a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a kasar nan.

 

Babban Jamiā€™in bankin a Jihar Ribas, Maxwell Okafor, ne ya yi zargin a Fatakwal, babban birnin Jihar lokacin da ya jagoranci ayarin CBN yayin ziyarar duba yadda bankuna da kasuwannin Jihar ke taā€™ammali da sabbin kudaden a ranar Jumaā€™a.

 

Ya ce tsakanin ranakun Alhamis da Jumaā€™a kawai, CBN ya ba bankunan kasuwancin da ke jihar tsabar kudin da suka kai Naira biliyan hudu da rabi, inda ya nuna damuwa kan yadda har yanzu jamaā€™a ba sa samun su.

 

Shi ma Daraktan Tsara Manufofi na bankin, Emenike Chimele, ya ce ko shakka babu wasu daga cikin bankunan na kokarin yi wa CBN zagon kasa kan sabuwar manufar.

 

Idan za a iya tunawa, CBN ya tsayar da 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin kudaden kwata-kwata a Najeriya.

 

Sai dai yayin da ya rage ā€™yan kwanaki kafin cikar waā€™adin, har yanzu mutane ma kokawa kan karancin sabbin takardun, yayin da har yanzu wasu bankunan da injinan ATM ke ci gaba da bayar da tsofaffin takardun.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...