Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNDLEA ta lalata gonar wiwi a jihar Ekiti

NDLEA ta lalata gonar wiwi a jihar Ekiti

Date:

Hafsat Iliyasu Dambo

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta lalata wata gona da aka shuka tabar wiwi mai fadi a jihar Ekiti.

 

Gonar na cikin wani daji ne da ke Ire Ekiti a karamar hukumar Oye.

 

Bayan gano wannan gonar ce jami’an na NDLEA suka lalata dukkan abin da ke cikin gonar.

 

Da yake yi wa manema labarai bayani, jim kadan bayan samun wannan nasara, mataimakin kwamandan hukumar ta NDLEA, na jihar Ekiti Mohammed Ibrahim, ya ce, yanzu haka sun samu nasarar kama mutum takwas wadanda ake zarginsu da sa hannu a wannan gona.

 

Kamar yadda Ibrahim ya bayyana sun kama tabar wiwin mai nauyin kilogram 1,465, sannan sun kama mutum takwas da ke da alaka wannan taba.

 

Yace yanzu haka ana ci gaba da bincike, domin gano wasu wuraren in akwai su.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...