Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan sanda sun kama barayin da suka saci takalmi a Ekiti

‘Yan sanda sun kama barayin da suka saci takalmi a Ekiti

Date:

‘Yan sanda a jihar Ekiti sun kama mutum biyu Olamide da Michael kan zargin sata takalma da fasa gidaje 16 da kantina a Ado Ekiti babban birnin jihar.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Sunday Abutu, ya fitar ranar Litinin.

 

Sanarwar ta ce kama Olamide da aka yi ne ya kai su ga kamo Michael, an kuma yi nasarar gano kayayyakin da suka sata a gidajen mutanen da suka kai korafin anyi musu sata.

 

A cewar sanarwar an samu kayan lantarki daban daban da takalma na maza da mata 220 a  maboyar baryin.

 

Haka kuma an samu kayan sawa na maza da mata 275 da barasa masu tsada da kayan masarufi da dai sauran abubuwa.

 

Sunday Abutu ya kara da cewa, “ya yin da ake ta kokarin kama wadanda suka tsere ne aka gano wadannan kayan, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su gaban shari’a.

 

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...